Connect with us

Labarai

Gwamnatin Tarayya: Buhari Ya Tsamo ‘Yan Najeriya Daga Kangin Talauci

 

Gwamnatin tarayya ta ce kalubalen tattalin arziki bai hana shugaban kasa Muhammad Buhari sanya murmushi a fuskokin talakawa da marasa galihu ba.

Nasir Sani-Gwarzo, babban sakatare na ma’aikatar kula da al’amuran jin kai, magance bala’o’i da ci gaban al’umma ne ya bayyana hakan, jiya a Jalingo, jihar Taraba, a lokacin kaddamar da shirin samar da ayyukan yi da kasuwanci na gwamnati, GEEP 2.0.

Sani-Gwarzo ya ce gwamnatin shugaba Buhari ta tsamo ‘yan Najeriya da dama daga ƙangin talauci, kuma har yanzu tana kan hanyar fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci kafin karshen gwamnatinsa a shekarar 2023.

“Tun da aka kafa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2015, a lokacin da ta gaji matakin talauci na kasa wanda ya kai kashi 70 cikin 100 na Hukumar Kididdiga ta Kasa, NBS, Gwamnatin Tarayya ta kara maida hankali wajen samar da mafita don magance matsalolin da ake fama da su akan talakawa da marasa galihu a kasar nan duk da wasu kalubalen tattalin arziki da gwamnatin ta gada a lokacin,” inji shi.

Ya kuma bayyana cewa an bullo da tsarin NSIP ne a shekarar 2015 a matsayin dabarar rage radadin talauci, kuma a halin yanzu tana samun hadin gwiwa da dama, ciki har da abokan huldar ci gaban kasa da kasa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet