Connect with us

Labarai

Yadda gwamna Ganduje ya gabatar da kasafin baɗi

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Ganduje, ya gabatar da kasafin baɗi da ya haura naira biliyan ɗari biyu da arba’in da biyar ga zauren majalisar dokoki domin dubawa tare da amincemasa yin amfani da shi.

Ganduje, ya gabatar da kasafin ne a yau Juma’a.

Yayin jawabinsa lokacin gabatar da kasafin, gwamnan ya ce, taken kasafin shi ne “Ɗorawa kan ayyukan ci gaba Karo na biyu”.

Hakan kuma ya ce, kasafin zai ƙarfafa tare da inganta rayuwar al’ummar jihar Kano la’akari da tanade-tanade da ke cikinsa.

Gwamna Ganduje ya ƙara da cewa, kasafin ya ƙunshi naira biliyan 144 da za a kashe wajen yin manyan ayyuka watau kimanin kashi 59 cikin 100 na kasafin, sai kuma naira biliyan 100 na kuɗaɗen da ake kashewa akai-akai.

Haka kuma a kasafin, an ware wa fannin lafiya Naira biliyan 39.1; albarkatun ruwa Naira biliyan 15; fannin sufuri Naira biliyan 8.6; fannin noma Naira biliyan 19.9 yayin da ayyuka da ababen more rayuwa suka samu Naira biliyan 35,” inji shi.

Gwamnan ya ce bangaren ilimi ya samu kaso mai dadi na kasafin kudi da Naira biliyan 62, wanda ya kai kashi 27 cikin 100 fiye da shawarar UNESCO da Majalisar Dinkin Duniya.

Ya Kara da cewar za a fitar da kudaden ne wajen aiwatar da manufofi da tsare-tsare da nufin tabbatar da ingantaccen ilimi a dukkan matakai.

Gwamna Ganduje ya ce za a kuma yi amfani da wani ɓangare na kuɗaɗen wajen inganta shirin ilimi kyauta kuma dole.

A jawabinsa bayan gabatar da kasafin, Shugaban majalisar dokoki Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari, ya bai wa gwamnan tabbacin yin gaggauta sahale kasafin da zarar sun kammala aikin a kansa.

Haka kuma Chidari, ya buƙaci ma’aikatun gwamnati da hukumomi da su kasance ciki shiri don kare kasafin a zauren majalisar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet