Ilimi
Gwamnatin tarayya- Kuɗin kwanakin da mambobin ASUU suka yi aiki muka biya ba rabi albashi ba
Gwamnatin tarayya ta musanta zargin cewa ta biya mambobin kungiyar malaman jami’o’i ASUU rabin albashin watan Oktoba.
Shugaban sashen yaɗa labarai na ma’aikatar ƙwadago da samar da ayyuka ta tarayya Mista Olajide Oshundun, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da fitar a ƙarshen makon nan.
Ya ce, adadin kwanakin da malaman suka koyar gwamnatin tarayya ta biya bayan janye yajin aiki ba wai rabin albashi aka biya ba.
Haka kuma, ma’aikatar ta mayar da martani akan kalaman shugaban kungiyar ta ASUU reshen jami’ar Usman Ɗan Fodiyo da ke Sokoto da suka zargi ministan ƙwadago da bayar da umarnin biyansu rabin albashi.
