Connect with us

Labarai

Kwamitin majalisar dokokin Kano ya kai ziyarar duba nagartar wasu manyan ayyuka

Mambobin kwamitin majalisar dokokin jihar Kano mai lura da yadda gwamnati ke kashe kuɗaɗen al’umma watau Public Account Committee PAC, sun kai ziyarar duba nagarta da gudanar wasu muhimman ayyukan da gwamnatin Ganduje ke yi a yanzu haka.

Kwamitin dai ya kai ziyarar ne da tsakar ranar yau Laraba ƙarƙashin jagorancin shugabansa Alhaji Salisu Ibrahim Muhammad wakilin mutanen ƙaramar hukumar Doguwa.

Mambobin kwamitin da suka kasance cikin tawagar sun haɗa da Mai tsawatarwa a majalisar Ayuba Labaran Durum wakilin Kabo da wakilin ƙaramar hukumar Nassarawa Umar Musa Gama da wakilin Wudil Nuhu Abdullahi Achika sai Hayatu Musa ɗorawar Sallau wakilin Kura/Garun Malam sai wakilin mazaɓar Rimin Gado/Tofa Muhammad Bello Ɓutu-ɓutu da wakilin ƙaramar hukumar Birni Salisu Maje Ahmad Gwangwazo sai wakilin Ɓagwai/Shanono Alhaji Ali Ibrahim Isa Shanono.

Baya ga Ƴan majalisar tawagar ta kuma ƙunshi wakilai daga ofishin PAC da kuma na ma’aikatar ayyuka da samar da ababen more rayuwa.

Ayyukan da kwamitin ya duba sun haɗa da aikin gina gadar sama da titin ƙarƙashin ƙasa na Hotoro da cibiyar kula da cutar sankara da gadar Ƙofar mata da ta shatale-talen Dangi.

Yayin da ya je jawabi ga manema labarai, shugaban kwamitin Alhaji Salisu Ibrahim Muhammad, ya bayyana gamsuwa dangane da yadda ayyukan ke gudana, yana mai cewa, sun gamsu da irin kayan da ƴan kwangilar suka yi aikin da su.

Haka kuma ya ce, “Wannan kwamiti yana da ikon duba dukkan wani aiki da gwamnati ke yi domin mu tabbatar da cewa ana kashe kuɗaɗen al’ummar jihar Kano yadda ya dace”

Shaba Abdurrazak, da ya yi magana a madadin kamfanin da ke gudanar da aikin gina cibiyar kula da cutar sankara watau Cancer, cewa ya yi, “Zuwa yanzu mun kammala fiye da kashi 90 na aikin da muke gudanarwa don haka za mu kammala shi nan da ƙarshen watan Nuwamban bana.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet