Labarai
Ana Zargin Wasu Bata Gari Sun Bankawa Ofishin Hukumar INEC Wuta
Wasu da ake zargin bata gari ne sun kona ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ke Iyana, a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
DAILY POST ta ruwaito cewa ‘yan ta’addan sun kai kimanin takwas, sun haure katangar, inda suka shiga harabar kuma suka cinna wa ginin INEC wuta daga baya.
An ce sun jika biredi da fetur sannan suka jefa guda cikin ginin ta kusurwoyi daban-daban don bankawa ofishin na INEC.wuta
Jami’in tsaron da ke wurin, Azeez Hamzat, ya kira ‘yan sanda da misalin karfe 1:00 na rana, inda ya ce ginin na ci da wuta.
Rundunar ‘yan sandan reshen Ibara ta ce ta tura jami’an tsaro zuwa wurin, tare da jami’an kashe gobara, domin kashe gobarar.
An tattaro cewa, ofishin jami’in mai kula da yiwa jama’a rijista da dakin taro ne gobarar ta shafa.
Hakazalika wata majiya ta shaida wa wakilin cewa gobarar ta shafa wasu kayayyaki.
“Babu wani rai da aka rasa kuma ba a samu rauni a gobarar ba” DAILY POST ta nakalto.
