Labarai
Kwamitin yaƙi da haramtattun gine-gine ya rushe wani gini a unguwar Kundila
Kwamitin kula da haramtattun gine-gine da aka yi ba bisa ƙa’ida ba a ƙarƙashin jagorancin Baffa Babba Dan’agundi ya amince da rushe wani gini da aka yi ba bisa ƙa’ida ba a unguwar Kungila.
Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar KAROTA Nabilusi Abubakar Ƙofar Nai’sa ya fitar a yau Alhamis.
Sanarwar ta ce, “Al’ummar unguwar ƙarƙashin jagorancin Dattijo Alhaji Abubakar Usman ne suka shigar da ƙorafinsu ga gwamnatin jihar Kano ta hannun shugaban kwamitin kula da gine-ginen da aka yi su ba bisa ka’ida ba Alhaji Baffa Babba Dan’agundi”.
Bayan binciken da kwamitin ya gudanar ya gano an yi ginin a kan hanyar magudanar ruwa wanda hakan ke zama barazana ga muhallin al’ummar unguwar ta Kundila.
“Shugaban Kwamitin Baffa Babba Dan’agundi ya ce, ba za su zuba ido suna gani wasu na amfani da damarsu ta aiki suna cutar da al’umma ba,” a cewar sanarwar.
Ya ce tuni mai girma Gwamnan ya bayar da umurnin a rushe wannan gini, sannan kwamitin ya ci gaba da sa-ido a unguwar Kwangila domin ganin ba a ci gaba da gine-ginen magudanar ruwa ba.
Baffa Babba ya ce Mai Girma Gwamnan ya bayar da umurnin bincike tare da gano waɗanda suke da hannu wajen bayar da shaidar yin gini a wajen domin ɗaukar matakin ladabtarwa a kansu.
Haka kuma sanarwar ta ce, Kwamitin ya jagoranci rushe ginin kamar yadda gwamnan Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar da umarni.
A ƙarshe shugaban kwamitin, ya ja hankalin al’ummar unguwar ta Kundila da su ci gaba da gyara magudanar ruwa domin gudun samun ambaliyar
ruwa a unguwannin.
