Labarai
Sojoji sun yi nasarar kashe ƙasurgumin ɗan bindiga Dogo Maikasuwa
Dakarun soja a jihar Kaduna, sun yi nasarar hallaka ƙasurgumin ɗan bindigar nan da ya addabi yankunan Birnin Gwari da jihohin Katsina da Neja da Kuma jihar Zamfara mai suna Dogo Maikasuwa.
Kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin masarautu na jihar ta Kaduna Mista Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan ga manema labarai da yammacin yau Juma’a.
Aruwan, ya ce sojojin sun kashe ɗan ta’addar ne a yankin karamar hukumar Chikun.
