Labarai
Jami’an ‘Yan Sanda Sun Tsaurara Tsaro A Kewayen Ofisoshin Hukumar Zabe
Rundunar ‘Yan sanda a Bauchi sun kara tsaurara matakan tsaro a kusa da ofisoshin hukumar zabe ta INEC a jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Ahmed Wakil, ya bayyana a ranar Lahadi a Bauchi cewa, an umurci jami’an ‘yan sanda na shiyya-shiyya da kwamandojin yankin da su tabbatar da shirin girke jami’an a ofisoshi da cibiyoyin INEC.
Ya kara da cewa hakan na da nufin karfafa tsaro da kuma ci gaba da sanya ido a yankunan da suke.
Ya kuma ba da tabbacin cewa ‘yan sanda za su yi aikin da aka dora musu na samar da yanayi mai aminci da kuma dacewa don gudanar da zabukan 2023 da ma sauran su.
Jaridar DailyNigerian ta rawaito cewa Mista Wakil, Sufuritandan ‘yan sanda, ya kuma bayyana cewa, ‘yan sandan za su ci gaba da samar da daidaito ga dukkanin ‘yan siyasa tare da ci gaba da kasancewa masu kwarewa wajen gudanar da ayyukansu.
“A bisa umarnin babban sufeto Janar na ‘yan sanda, Mista Usman Baba, kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, Umar Sanda ya baza jami’ai don gudanar aiki kewaye cibiyoyin INEC.
“Wannan shi ne don ayyukan sa ido da bincikar ayyukan aikata laifuka da kuma samar da yanayi mai kyau don aiwatar da ayyukan siyasa ba tare da matsala ba.
“Wadannan tura jami’ai an yi su ne da nufin sanya ido kan kayan aiki da kayan INEC da kuma hana duk wani yunƙuri na barakar tsaro a kusa da su da kuma daidaita martanin da ya dace game da kiran gaggawa,” in ji shi.

Deschidere cont Binance
03/07/2023 at 2:29 pm
Your article helped me a lot, is there any more related content? Thanks! https://accounts.binance.com/ro/register?ref=V3MG69RO