Kasuwanci
IPMAN Ta Yi Allah Wadai Da Biyan Tallafin Man Fetur Wanda Ba Mai Dorewa Ba
Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Kasa (lPMAN), ta ce tallafin da ake bayarwa kan man Motoci, wanda aka fi sani da fetur, ba ya dawwama.
Mista Mike Osatuyi, Kwanturolan ayyuka na kasa na lPMAN, a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) a ranar Litinin a Legas, inda ya yi Allah wadai da biyan tallafin man fetur.
Osatuyi ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun karin farashin man fetur a gidajen mai a fadin kasar nan.
Ya ce gwamnatin tarayya ta kashe Naira tiriliyan 20.51 a kasafin kudin shekarar 2023 sabanin kudaden shiga na Naira tiriliyan 9.7, inda ya bar gibin Naira tiriliyan 10.78.
Osatuyi ya ce gwamnati na fatan bayar da tallafin man fetur har zuwa watan Yunin 2023 kan kudi Naira tiriliyan 3.6, ta hanyar amfani da babban bankin Kasa (CBN) da ya kai Naira 435 zuwa dala daya.
“A halin yanzu, farashin a hukumance na CBN ya kai kusan Naira 445 a dala daya wanda ya haura Naira 435 zuwa dalar da aka yi hasashen a kasafin kudin shekarar 2023,” inji shi.
Ya ce tsarin bayar da tallafin ya haifar da karuwar gibin kasafin kudi tare da haifar da koma baya ga rancen tattalin arziki.
Ya kuma ce tallafin ya sa fasa-kwaurin man fetur ya zama sana’a mai fafutuka saboda ribar da ake samu.
