Yin gyara ga dokar ya biyo bayan amincewa da karatu na biyu da na uku a zaman majalisar na yau Litinin.
Majiyar mu ta ruwaito cewa yayin karatu na biyu na dokar, shugaban masu rinjaye a majalisar Alhaji Labaran Abdul Madari, ya bayyana cewa an kara shekarun ritayar malamai daga shekaru 60 zuwa 65 yayin da aka duba shekarar aiki daga shekaru 35 zuwa 40.
Bayan haka ne kuma majalisar ta umurci magatakardanta Alhaji Garba Bako Gezawa da ya gabatar da karatu na uku na dokar.
Haka kuma, Bayan tattaunawa na tsanaki ne majalisar ta amince ta gyaran sashe na 14 na dokar fansho da giratuti ta jihar Kano na shekarar 2006.
