Connect with us

Labarai

2023: IG Na Yan Sanda Ya Zargi Wasu Gwamnoni Da Kitsa Rikicin Siyasa

Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Kasar nan, Mista Usman Baba, ya dora alhakin karuwar rikice-rikicen siyasa da ake samu a kasar kan wasu gwamnonin jihohi.

Baba ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi da shugabannin jam’iyyun siyasa da sauran masu ruwa da tsaki a ranar Alhamis din nan a Abuja.

Ya ce an kira taron ne domin jan hankalin shugabannin jam’iyyun siyasa kan yadda ake samun karuwar rikicin siyasar da kuma gabatar da yadda za a magance matsalolin.

“Muna ta samun rahotannin wasu Gwamnonin Jihohi da ke karfafa ‘yan barandan siyasa.

“Suna amfani da kayan tsaro na kananan hukumomin da ke karkashinsu domin dakile ayyukan yakin neman zabe na jam’iyyu ko ‘yan takarar da suke da sabanin ra’ayi na siyasa.

“A don haka, suna amfani da ikonsu da tasirinsu don hana yakin neman zabe ko kuma su ruguza su.

“Suna kuma hana ‘yan adawar siyasa gudanar da yakin neman zabensu ko ayyulansu na siyasa cikin lumana wanda ya saba wa tanadin dokar zabe ta 2022 (Kamar yadda aka gyara),” in ji shi.

IG ya ce ya dora alhakin mafi yawan tashe-tashen hankula a kan tsattsauran ra’ayi na siyasa, rashin fahimta, rashin hakuri, kuskuren siyasa, kalaman kiyayya, tunzura jama’a da kuma yanke kauna na wasu ‘yan siyasa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet