Connect with us

Labarai

Wata Kotu Ta Kori Karar Da Dan Takarar Gwamna Ya Shigar Kan Wanda Jam’iyya Ta Tsayar

Wata babbar kotun tarayya da ke zama a babban birnin tarayya Abuja, ta yi watsi da karar da Honarabul Sani Idris Kutigi ya shigar kan Honarabul Isah Liman Kantigi, wanda ya lashe zaben fidda gwanin gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Neja.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Daraktan Sadarwa na kwamitin Yakin neman zaben PDP na Jihar Neja, Usman Mohammad Yahaya da mai taimaka wa kan harkokin yada labarai, Comrade Israel kolo, a Minna.

A cewar sanarwar, wanda ya sha kaye a hannun Kantigi, ya shigar da karar yana neman a soke Kantigi a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar a zaben 2023 a kotun tarayya da ke Abuja.

A cewar sanarwar: “Shugaban alkalin kotun, Hon. Mai shari’a Zaynab Mohammed ta ce Hon. Sani Idris Kutigi ba shi da wani dalili na daukar mataki don haka, saboda haka, an “kori karar.”

Kantigi ya doke wasu ’yan takara hudu inda suka samu tikitin takarar jam’iyyar a zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka gudanar a ranar 26 ga watan Mayu, 2022. Wadanda suka yi takarar sun hada da Sani Idris Kutigi, Sidi Abdul Gulu, Barista Abdulrahman Gimba da Engr Abubakar Isah Jankara.

Kantigi ya samu kuri’u 667 daga cikin kuri’u 808 inda ya zama wanda ya lashe zaben, yayin da abokin hamayyarsa Sani Idris Kutigi ya samu kuri’u 114. Isah Jankara da Gimbal Abdul Rahman sun samu kuri’u 21 da kuri’u 3 yayin da Alh Sidi Abdul bai samu ko kuri’a ba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet