Kasuwanci
CBN Ya Umarci Bankuna Da Su Rika Yin Aiki A Ranakun Hutun Karshen Mako
Babban bankin Najeriya CBN ya umurci bankunan kasuwanci a kasar da su dinga yin aiki a ranakun Asabar har zuwa ranar 31 ga watan Junairu, 2023, domin baiwa kwastomomi damar dawo da takardun Naira da suke da su.
Babban bankin na CBN ya bayyana shirin sake fasalin takardun kudi na N200, N500, da N1,000, tare da fitar da sabbin takardun kafin ranar 15 ga watan Disamba, 2022.
Da yake jawabi a wajen bikin baje kolin na CBN a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, ranar Alhamis, Daraktan CBN, Sashen Sadarwa, Osita Nwasinobi, ya ce sabbin takardun da ake da su za su ci gaba da kasancewa a kan doka har zuwa ranar 31 ga watan Janairu, 2023, lokacin da takardun da ake da su za su daina aiki.
Taken Baje kolin na CBN,shine “Samar da daidaiton harkokin kudi da bunkasar tattalin arziki.”
Daraktan wanda ya samu wakilcin mukaddashin daraktan Sadarwa na CBN, Akpama Uket, ya bayyana hakan cewa an umurci bankunan ajiya da su gaggauta dawo da kudaden da ake da su ga CBN.
“An kuma umurce su da su karɓi takardun kuɗin da ake da su fiye da yadda tsarin Cashless ya tsara ba tare da cajin abokan ciniki ba.
“Saboda haka, dole ne ku dawo da duk takardun kudi na N200, N500, da N1,000 na yanzu zuwa bankin ku kafin cikar wa’adin,” inji shi.
A halin da ake ciki, CBN ya gargadi ‘yan Najeriya kan illar karkatar da takardun kudin Naira, inda ya ce, “Bari ni ma na nanata bukatar a kula da Naira da kyau. Naira ta ci gaba da zama alamar abin alfaharinmu. Ku bi shi da matuƙar daraja.
“Kada ku fesa, matse ko yin jabun naira, saboda gazawar tana da sakamako.”
