Featured
Ƴan wasan ƙasar Ecuador sun lallasa Qatar mai masaukin baƙi da ci 2 – 0
Tawagar ƙwallon ƙafa ta kasar Ecuador ta lallasa tawagar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Qatar a wasan farko na gasar cin kofin Duniya wanda Qatar ɗin ta karɓi baƙuncinsa.
Ƙasar Ecuador, ta samu nasarar ne ta hannun ɗan wasanta E. Valencia wanda ya zura duka kwallayen biyu tun a zagayen farko na wasan wanda aka fara shi da yammacin yau Lahadi.
Sai dai bayan Ecuador ta yi nasarar samun ƙwallayen biyu an tashi ne ba tare da Qatar ta zura ko da ƙwallon ɗaya ba.
