Labarai
Murnar doke Argentina: Sarki Salman bin Abdul Aziz ya ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu
Sarki Salman bin Abdul Aziz na Saudiyya, ya ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu a faɗin ƙasar wani mataki na murnar samun nasara da tawagar ƴan wasan ƙwallon ƙafar ƙasar suka samu a kan ƙasar Argentina.
An dai tashi wasan ne Saudiyya ta samu nasara a kan Argentina da ci 2-1 a wasan farko da suka buga a filin wasa na Lusail.
Ƙasar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanar wa da ta fitar a yau Talata.
Sanarwar ta ce, Sarkin ya bayar da hutun ne domin ƴan ƙasar tun daga ma’aikatan gwamnati da ma’aikatu masu zaman kansu har ma da ɗaukacin ɗalibai su gudanar da murnar nasarar da tawagar ƴan wasan ƙasar ta samu kan ƴan wasan ƙasar Argentina a gasar ƙwallaon ƙafa ta cin kofin duniya da ake gudanarwa a ƙasar Qatar.
