Labarai
Allah ya yi wa limamin Masallacin Quba na Madina rasuwa
Allah ya yi wa limamin Masallacin Quba da ke birnin Madina Sheikh Muhammad Abid Al-Sindi, rasuwa.
BBC ta ruwaito cewa, Shafin Twitter na Haramain Sharifain ne ya wallafa labarin rasuwar limamin.
Haka kuma Shafin ya bayyana cewa, tuni aka gudanar da jana’izar marigayi Sheikh Abid Al-Sindi, inda aka binne shi a makabartar Baqee da ke birnin na Madina.
Haka kuma ta ruwaito cewa, a baya marigayi yana jagorantar Sallar tarawih ne a Masallacin Manzon Tsira, kafin daga bisani ya koma masallacin na Quba.
