Connect with us

Kasuwanci

Shugaba Buhari Ya Kaddamar Da Aikin Hako Mai Na Farko A Shiyyar Arewa Maso Gabas

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talatar nan ya kaddamar da shirin ci gaba na Kolmani a shiyyar Arewa maso Gabas, wanda shi ne irinsa na farko a shiyyar.

Buhari ya ce aikin hakar mai a kogin Kolmani da ke tsakanin jihohin Gombe da Bauchi ya riga ya jawo jarin waje na sama da dala miliyan 3, kuma zai bunkasa arzikin Najeriya da kuma samun kudin shiga.

Ana sa ran fara aikin da hako danyen mai kusan ganga 50,000 a kullum.

Taron ya samu halartar shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan; dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu; Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Slyva; da babban jami’in rukunin kamfanin mai na Najeriya (NNPC) Limited, Mele Kyari;

Sauran sun hada da Gwamna Bala Mohammed (Bauchi), Inuwa Yahaya (Gombe), Simon Lalong (Plateau). Babban Manajin Darakta na Kamfanin Cigaban New Nigeria, Shehu Mai-Borno shi ma ya halarci taron.

A shekarar 2019 ne hukumar NNPC ta sanar da gano danyen mai a yankin kogin Kolmani da ke kan iyakar jihohin Bauchi da Gombe.

Bayan haka, sashe na 9 na dokar masana’antar man fetur (PIA) da shugaban kasa ya sanya wa hannu ya kafa Asusun Hako Man Fetur (FEF) tare da kasafta kashi 30 na ribar da kamfanin NNPC ke samu daga kwangilolin mai da iskar gas da nufin hako mai a Kolmani haka ma Anambara, Dahomey, Bida, Chad da Benue Trough.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet