Labarai
Borno: Sojojin sama sun hallaka ƴan Boko Haram 16 a luguden wuta
Dakarun Sojojin Sama sun samu nasarar kashe mambobin ƙungiyar Boko Haram goma sha shida a farmaki da jirgin yaƙi samfurin Super Tucano ykai musu a yankin Banki da ke kan iyaka da ƙaramar hukumar Bama ta jihar Borno.
Daily Trust ta ruwaito cewa Dakarun sun samu nasarar ne a ranakun 16 da 17 ga wannan watan da muke ciki na Nuwamba.
Haka kuma ta ƙara da cewa, bayan harin sojojin sama wani ƙwararre a fannin yaki da tayar da kayar baya, a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama, a karshen mako a birnin na Maiduguri, ya ce, “Boko Haram ta sake samun wata mummunan asara a aikin hadin gwiwa na sojojin hadin gwiwa a yankunan Banki.”
