Labarai
Allah ya yi wa fitaccen ɗan jarida Bashir Mohammed Baba rasuwa
Allah ya yi wa tsohon fitaccen ɗan jarida kuma manazarci a harkokin gidajen rediyo da talabijin Malam Bashir Mohammed Baba rasuwa.
Rahotonni sun ce ya rasu ne da sanyin safiyar yau sakamakon raunukan da ya samu a cikin bandakinsa.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Bashir Baba ya rasu a safiyar yau Asabar a Abuja.
Bashir Baba gogaggen dan jarida ne sama da shekaru arba’in wanda ya fara aiki da NTA, manazarci ne a BBC, VOA, DW-Radio da kuma Prestige Radio dake Minna, shirin ‘Kasar Mu a Yau’ da kuma shirin Idon Mikiya na Farin Wata Television da Vision FM
Ya fara shirye-shiryen kasar mu ayau a Liberty Television. Ya kuma kasance Babban Mataimakin Mai Watsa Labarai Ma’aikatar Harkokin Waje a karkashin Ambasada Aminu Bashir Wali.
Tuni dai a yau Asabar aka yi jana’izarsa a garin Wudil da ke Kano.
