Labarai
INEC Ta Fitar Da Wasu Ka’idoji, Tare Da Haramta Gangami A Wuraren Ibada
Yayin da babban zaben shekarar 2023 ya rage watanni uku, Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) ta fitar da wasu ka’idojinta na gudanar da harkokin siyasa.
Hukumar, a cikin wata takardar sanarwa mai shafuka shida mai taken “Halin taron siyasa, Taro da yakin neman zabe,” ta haramta amfani da kalaman batanci da kalaman kyama da kuma yakin neman zabe da gangamin siyasa a wuraren ibada.
Haka kuma an bayyana cewa an haramtawa duk wanda zai halarci gangamin siyasa ko gangamin yakin neman zabe ya mallaki duk wani makami mai ban tsoro.
Wadanda kawai aka ba su izinin daukar makamai a irin wannan taron, a cewar INEC, su ne jami’an ‘yan sanda ko jami’an tsaro da aka sanya musamman domin halartar tarukan siyasa ko jerin gwano.
“Ba za a yi gangamin siyasa ba a wuraren da aka keɓe a matsayin cibiyoyin addini, ofisoshin ‘yan sanda da ofisoshin gwamnati.
“yakin neman zaben siyasa ba zai amince da amfani da kalaman batanci ko kowane irin kalaman ƙiyayya ba.
“Ba za a yi amfani da na’urorin gwamnati da suka hada da kafafen yada labarai don amfanin kowace jam’iyya ko dan takara a kowane zabe ba,” in ji shi.
Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa INEC ta lura cewa, makasudin gudanar da gangamin siyasa shi ne tsarawa, bayarwa, wayar da kan jama’a game da alamar jam’iyyar, tuta, taken jam’iyyar, da kuma takardar manufofi.
