Labarai
Gwamnatin Bauchi ta ƙaddamar da cibiyar koya wa matasa sana’o’i da tace man fetur
Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed Abdulƙadir, ya ce gwamnatinsa ta kafa cibiyar horas da matasa ƙere-ƙere da harkokin tace man fetur.
Gwamnan, ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da sashe Hausa na BBC.
Ya ce, Sunan cibiyar Alkaleri Oil and Gas Acquisition Centre, kuma tuni gwamnatin tasa ta ƙaddamar da ita.
Haka kuma, Ya ƙara da cewa jihohin arewacin Najeriya sun zuba jarin da ya kai kusan dala miliyan 10 a aikin haƙo man fetur ɗin da aka gano a kan iyakar jihohin Bauchi da Gombe.
Gwamna Bala Muhammad Abdulƙadir, ya kuma ce, kamfanin ya samu tallafi daga kamfanin mai na ƙasa NNPCL har ma da wasu kamfanonin man fetur na ƙasashen ƙetare.
