Connect with us

Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Wajabta Amfani Da NIN Ga Fasinjojin Abuja Zuwa Kaduna

 

Gabanin shirin dawo da zirga-zirgar jiragen kasa daga Abuja zuwa Kaduna, gwamnatin tarayya ta ce dole fasinjojin da zasu hau jirgin su yi rajistar lambobin wayarsu da lambar shaidar kasa (NIN) a wurin siyan tikitin.

Gwamnati ta hannun hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta Kasa NRC, ta ce za a girke na’urorin tantance fasinja a kowace tashar jirgin kasa da ke kan hanya domin jami’anta su tabbatar da sahihancin fasinjojin.

Hukumar NRC ta kuma yi gargadin cewa yana da hadari ga duk wani dan Najeriya ya yi amfani da NIN din sa wajen siyan tikitin ga wadanda ba a san ko su waye ba domin hakan na iya kaiwa ga gurfanar da su a gaban kotu.

Ministan Sufuri, Mu’azu Sambo a ranar 7 ga Nuwambar, 2022 ya sanar da cewa za a ci gaba da zirga-zirgar jiragen kasa na layin dogo daga Abuja zuwa Kaduna a cikin watan Nuwamba, inda ya ce an samar da isasshen tsaro don tabbatar da lafiyar fasinjoji.

Tashar talabijin ta Channels ta rawaito cewa Ministan ya ce gwamnati ta koyi isassun darussa daga harin da aka kai a watan Maris wanda ya kai ga dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa kan hanyar Abuja zuwa Kaduna amma bai bayar da takamaiman ranar da za a ci gaba da aikin ba.

Jaridar Alkiblah ta rawaito cewa Hukumar NRC ta dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa a kan hanyar bayan da ‘yan ta’addar Boko Haram suka kai wa wani jirgin fasinja hari a Kaduna a ranar 28 ga watan Maris, 2022.

Maharan sun tarwatsa titin jirgin tare da jefa bam a cikin jirgin da ke tafiya, inda suka kashe wasu tare da yin awon gaba da fasinjoji sama da 60.

Harin da ba a taba yin irinsa ba ya janyo cece-ku-ce tsakanin kasashen duniya da na kasar baki daya.

‘Yan ta’addan, wadanda suka kai hari kan jirgin kasa a Kaduna, sun sako mutanen da aka yi garkuwa da su ne a ranar 5 ga Oktoban 2022.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet