Connect with us

Labarai

Shugaba Buhari Ya Bada Tabbacin Gudanar Da Sahihin Zabe Ga Shugbannin ECOWAS

 

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tabbatarwa da shugabannin kungiyar ECOWAS cewa za su gudanar da zabe na gaskiya da adalci a cikin watan Fabrairu.

Za a gudanar da babban zabe a Kasar nan a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 na shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa da ‘yan majalisar dattawa da na wakilai.

Jaridar Alkiblah ta rawaito cewa Shugaba Buhari mai ci ba zai iya tsayawa takara ba, kasancewar ba shi da damar haka bisa tana din kundun tsarin mulki.

Buhari ya bayyana haka ne a wajen bude taro na biyu na majalisar ECOWAS na shekarar 2022 a Abuja da ke zaman nazarin shawarwarin kudi na 2023 na al’umma.

Ya ci gaba da cewa, “Yayin da ake sa ran wannan zama na biyu na majalisar ECOWAS zai yi la’akari da kasafin kudin al’umma da dai sauransu, bari in jaddada cewa tabarbarewar tattalin arzikin duniya ya yi matukar tasiri ga tattalin arzikin yankinmu, ya kuma jawo wa ‘yan kasar tabarbarewar tattalin arziki.

“Saboda haka, ina kira gare ku da ku aiwatar da aikinku mai tsarki bisa yin la’akari da kasafin kudin al’umma da himma, tare da la’akari da sadaukarwar da kasashe daban-daban suka yi wajen biyan harajin Community Levy.

“Ina kira gare ku da ku lura da dimbin kalubalen da ya yiwa yankin kawanya, ku kuma kula da bukatun jama’a.”

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa Shugaban ya kuma yabawa shugaban majalisar ECOWAS, Dokta Sidie Tunis, bisa irin jajircewa da sadaukarwa da yake bayarwa wajen inganta dunkulewar yankin da karfafa dimokuradiyya da shugabanci na gari a yankinmu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet