Connect with us

Labarai

Wata Babbar Kotu Ta Yankewa IGP Hukuncin Dauri A Gidan Yari

 

Mai shari’a Mobolaji Olajuwon na babbar kotun tarayya da ke zaman ta Abuja, ya yanke wa babban Sufeto Janar na ‘yan sanda IGP, Usman Baba hukuncin daurin watanni uku a gidan yari saboda ya ki bin umarnin kotu.

Da yake yanke hukunci, Mai shari’a Olajuwon ya bayar da umarnin ne biyo bayan karar da wani tsohon jami’in ‘yan sanda, Patrick Okoli ya shigar inda ya ce ya yi ritaya daga aikin ‘yan sandan Najeriya ba bisa ka’ida ba.

A cewar sanarwar da ke nuna goyon bayan karar, mai neman (Okoli) ya yi ritaya ta karfi a watan Yunin 1992.

Jaridar Alkiblah ta rawaito cewa A ranar 19 ga watan Fabrairun 1994, wata babbar kotun Bauchi ta kalubalanci murabus dinsa taa karfi, ta yanke hukunci a kan wanda ya nema tare da soke takardar murabus din na dole.

Babbar kotun ta kuma bayar da umarnin mayar da mai neman aiki tare da biyansa duk wani hakkinsa na karin girma .

Hukumar da ke kula da aikin ‘yan sanda (PSC) a wata wasika mai dauke da kwanan watan 13 ga watan Oktoba, 2004, ta umurci IGP na lokacin da ya dawo da mai karar tare da bayar da shawarar karin girma kamar yadda kotu ta yanke.

Don haka, Okoli ya shigar da kara mai lamba FHC/ABJ/CS/637/2009 a babban kotun tarayya da ke Abuja yana neman a ba shi umarnin tilasta aiwatar da umarnin babbar kotun Bauchi da kuma umarnin PSC.

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke hukuncin ne a kan wanda ya shigar da karar a ranar 21 ga watan Oktobar, 2011.

Ofishin IGP ya daukaka kara kan hukuncin kotun amma aka yi watsi da karar.

Mai neman kara daukar matakan aiwatar da wannan umarni da suka hada da tunkarar majalisar wakilai ta tarayya inda daga nan ne ya rubutawa ofishin IGP din.

Tashar talabijin ta Channels ta rawaito cewa Bayan kokarin ya ci tura, mai neman ya tuntubi lauyan Festus Keyamo, don fara ci gaba da shari’ar wanda ake kara.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet