Labarai
An Sace Kayan Ango, Yayin Da Sadaki Ya Bata A Wajen Daurin Aure
Al’ummar unguwar Fagge Quarters da ke karamar hukumar Tarauni a jihar Kano har yanzu ba su farfaɗo ba, bayan da wani ango ya yi asarar kayan sawar aure da kuma sace sadakin amaryar sa sa’o’i 24 kafin ɗaurin aurensa.
Angon da ya nemi a sakaya sunansa ya rasa tufafin kayan sawar da ya ajiye don ya sa.
Lamarin da ya afku a ranar Asabar din da ta gabata ya sanya ango da iyalansa cikin rudani sakamakon yadda ya yi aiki tukuru wajen ajiye kudi da sayen wadanda kayan da suka bata.
“Yanzu me zan sa na wannan bikin sau ɗaya a rayuwa? Ya tambaya.
Angon ya kai karar hukumar ‘yan sanda dake Tarauni, inda suka fara bincike a kai.
Mafi muni kuma, an saci kudin sadakin amarya a wurin daurin auren. An samu rudani lokacin da aka gano cewa an sace kudin sadakin.
Ana bukatar shigar dattijai a wajen bikin don kwantar da hankulan daga baya kuma a amince cewa a daura auren da alkawarin cewa za a biyan kudin sadakin amarya daga baya, abin da ake kira ‘Ajalan’ wato bashi.
Wani Abdussalam da ya shaida lamarin ya ce abin kunya ne matuka, don haka ya yi kira ga jama’a da su yi taka tsantsan da irin wadannan makudan kudade.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su ji tsoron Allah su daina yin abubuwan da ke nuna jihar Kano da mummunan hali.
Jaridar Leadership ta rawaito cewa, Shima da yake tsokaci, wani matashi mai suna ‘Yan Bita’ ya ce ya kadu matuka da faruwar abubuwa biyu marasa dadi, inda ya ce da a ce yana da kudi da ya sake siyo wa ango wani kayan ya hada da kudin sadakin amaryar da aka sace.
