Labarai
INEC: Babu Muhimman Kayan Da Suka Lalace A Harin Da Aka Kaiwa Ofishin Hukumar Zabe
Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) ta ce babu daya daga cikin muhimman kayayyakin zabe da aka lalata a harin da aka kai ofishinta da ke Owerri, babban birnin jihar Imo a ranar Litinin din nan.
Hukumar a cikin wata sanarwa da kwamishinanta na kasa kuma shugaban kwamitin wayar da kan jama’a da wayar da kan masu kada kuri’a Festus Okoye ya fitar, ya kuma tabbatar da cewa babu wani ma’aikacin hukumar da ya rasa ransa a lamarin wanda ya ce ya faru da misalin karfe 3:00 na daren ranar Litinin.
Sai dai sanarwar ta ce harin ya shafi bangaren ginin da ke da ofishin sa ido kan zabe da bibiya (EPM) ke ciki, an kuma kona wata motar amfanin jami’ai (wata mota kirar Toyota Hilux).
Jaridar Alkiblah ta rawaito cewa, wannan shi ne karo na uku da aka kai wa cibiyoyin hukumar a jihar Imo cikin kasa da makwanni biyu bayan harin da aka kai a ofishinta na karamar hukumar Orlu a ranar Alhamis 1 ga watan Disambar 2022 da ofishin karamar hukumar Oru ta Yamma a ranar Lahadi 4 ga watan na Disamba 2022.
Hukumar ta bayyana lamarin a matsayin wani sabon hari da aka kai kan kadarorinta a fadin kasar, fiye da ranar da aka fara karbar katin zabe na dindindin a duk fadin kasar gabanin babban zaben 2023.
A harin baya-bayan nan da aka kai kan wata cibiyar INEC a jihar Imo, an kashe mutane hudu ciki har da dan sanda guda daya a shedikwatar hukumar da ke kan hanyar Fatakwal.
A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Imo, Mike Abattam, ‘yan bindigar da yawansu ya haura 10 sun zo da misalin karfe 3:00 na dare dauke da bama-bamai na fetur da kuma dinamite.
Sai dai ya ce ‘yan ta’addan sun yi karo da jami’an tsaro wadanda suka dakile harin tare da kashe uku daga cikin maharan.
Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa, Abattam ya kuma ce ‘yan sanda sun kama daya daga cikin maharan sannan an kwato motoci uku da ‘yan fashin ke amfani da su.
