Connect with us

Labarai

Rundunar Yan Sanda A Sokoto Ta Gargadi ‘Yan Siyasa Su Guji Aikata Laifuka

 

Gabanin zaben shekarar 2023, kwamishinan ‘yan sandan jihar Sokoto, Muhammed Usaini Gumel, ya ja hankalin jama’a da su taka rawar da ta kamata, wajen ganin an tabbatar da daidaito a tsakanin masu zabe, da ‘yan takarar da ke neman mukamai daban daban a zabe 2023.

Kwamishinan a wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar, Sanusi Abubakar, ya kara gargadin ‘yan siyasa da su guji aikata laifuka a yayin zabe.

Wasu daga cikin laifukan zaben a cewar Gumel sun hada da kada kuri’a da wadanda ba su yi rijista ba da kuma kada kuri’a a boye.

Sauran sun hada da sayen kuri’a ko siyarwa da kudi, rashin daidaito a rumfunan zabe, jefa kuri’a ba daidai ba da sanarwa ta karya, barazanar kai tsaye ko ta kaikaice tare da tashin hankali don tilastawa ko hana masu kada kuri’a ko wata ‘yanci yayin zabe, tasirin da bai dace ba.

Sauran su ne kwacewa ko lalata kayan zabe da kuma zamba cikin aminci a lokacin zaben, da dai sauran su.

Bisa la’akari da abubuwan da suka gabata, rundunar ‘yan sandan ta sake nanata aniyar ta na tunkarar wadanda suka karya doka bisa tanadin dokar zabe, da ta kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya da sauran wasu manyan dokoki.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet