Labarai
Kudurin Buhari Na Fitar Da ‘Yan Najeriya Daga Talauci Ya Karkata Kan Mata – Minista
Ministar harkokin jin kai da kula da bala’o’i da ci gaban jama’a, Hajiya Sadiya Umar Farouq ta bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta kudiri aniyar fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci nan da shekaru goma masu zuwa.
Alhaji Bello Alkali wanda ya samu wakilcin Darakta a ma’aikatar ya bayyana hakan a Birnin Kebbi a ranar Litinin din da ta gabata a wajen bikin bayar da tallafin kudi ga kungiyoyi marasa galihu da gwamnatin tarayya ta yi, karkashin shirin (GEEP) wanda ya hada da Marketmoni, Tradermoni da Farmermoni.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai baiwa gwamnan jihar Kebbi shawara, Yahaya Sarki, ya ce ministan ya nuna cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajirce sosai kan shirinsa na fitar da mutane daga kangin talauci nan da shekaru goma masu zuwa.
Ya kara da cewa mutane 4112 ne za su ci gajiyar shirin, wanda kashi 70 cikin 100 dole ne su kasance mata, sannan kashi 30 cikin 100 na matasa, yayin da aka mayar da hankali kan masu bukata ta musamman matasa, zawarawa, ‘yan gudun hijira da nakasassu da dai sauransu.
Ta bayyana shirin “Tradermoni, na tallafin N50,000 ga wadanda suka ci gajiyar shekaru 18 zuwa 40, Marketmoni na mata marasa galihu da kuma mai da hankali ga gidajen mata kamar matan da mazansu suka mutu da wadanda aka kashe.
Ita ma shugabar aiwatar da shirin na GEEP, Hajiya Zainab Musa ta ce GEEP na kai dubansa a yankunan karkara da ba su da damar samun kudi a zamance.
