Labarai
Tinubu Ya Daukarwa Masu Zabe Alkawarin Kawar Da Masu Garkuwa Da Mutane
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya yi alkawarin kawar da masu garkuwa da mutane da sauran ‘yan ta’adda da ke addabar jihar Kaduna a Arewa maso Yammacin Najeriya.
“Dukkan masu tayar da hankali, masu garkuwa da mutane, masu kashe mutane; duk masu tayar da hankali da ke sa(damuwa) tsaron Kaduna, ina tabbatar muku, za mu kawar da su,” in ji shi a taron yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC na Arewa maso Yamma a Kaduna ranar Talatar nan.
Jaridar Alkiblah ta rawaito cewa, Jihar Kaduna, daya daga cikin jihohi bakwai na shiyyar Arewa maso Yamma, ta sami karuwar hare-haren ‘yan bindiga da na ta’addanci a cikin shekaru biyu da suka gabata, ciki har da kutsawa cikin makarantar horas da sojoji ta Najeriya a ranar 24 ga watan Agustar 2021 da wani harin bam da aka kai kan wani jirgin kasa da ke tafiya a watan Maris 28, 2022.
Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ‘yan bindiga da wasu kungiyoyin masu tayar da kayar baya sun kashe mutane 1,192 a shekarar 2021 yayin da sama da mazauna, dalibai da matafiya sama da 3,000 suka yi garkuwa da su.
Ya zuwa yanzu, sama da mutane 800 ne ‘yan bindiga suka kashe tare da yin garkuwa da sama da mutane 1,200 a Kaduna tsakanin watan Janairu zuwa Satumbar 2022, kamar yadda bayanai suka nuna.
Sai dai kuma, Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas, ya shaida wa dimbin magoya bayan jam’iyyar APC da suka yi cincirindo da kayan jam’iyyar a ranar Talata cewa zai iya kawo karshen matsalolin tsaro a jihar.
Ya kuma ce gwamnan Kaduna mai ci, Nasir El-Rufai ya taka rawar gani tun bayan da ya hau mulki a shekarar 2015. Don haka ya bukaci jam’iyyar da ta yi amanna da su zabi kansa da dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a Kaduna, Uba Sani a zaben 2023 mai zuwa.
“El-Rufai ya yi aiki mai kyau, ka zagaya Kaduna, za ka ga yadda aka tsara, tsafta a (jihar). Ya fi samun kudaden shiga a cikin gida,” in ji Tinubu, inda ya yi alkawarin samar da ayyukan yi, amfani da damar noma da karfafawa matasa gwiwa idan aka zabe shi a ranar 25 ga watan Fabrairun 2022.
