Labarai
Majalisar Dattawa Ta Dage Yin Muhawara Akan Dokar Kayyade Fitar Da Kudi Ta CBN
Majalisar dattawa ta dage gudanar da muhawarar da ta shirya yi kan dokar cire kudaden da babban bankin Kasa CBN ya yi har zuwa ranar Laraba 14 ga watan Disambar 2022.
Hakan ya faru ne saboda rashin halartar shugaban kwamitin kula da harkokin bankuna da kudi, Sanata Uba Sani, wanda zai halarci taron gangamin jam’iyyar APC na kasa a Kaduna.
Wani mamba a kwamitin, Sanata Olubunmi Adetumbi, a cikin wata sanarwa ya shaida wa abokan aikinsa cewa dole ne a rufe rahoton da za a gabatar a zauren majalisar na ranar Talata saboda Sani ya halarci taron APC a Kaduna.
Adetumbi ya tabbatar wa majalisar dattijai cewa rahoton kwamitin kan dokar kayyade fitar da kudi ta CBN a shirye yake, inda ya ce dole ne shugaban kwamitin ya halarci taron jam’iyyar APC na shiyyar a matsayinsa na dan takarar gwamnan jihar Kaduna.
Da yake mayar da martani, Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya yi kira ga ‘yan majalisar da su yi hakuri domin za a bayyana sakamakon kwamitin a cikin sa’o’i 24.
Ana kuma sa ran Uba Sani zai yi wa takwarorinsa bayanin sakamakon tantance Edward Adamu da Aisha Ahmad a matsayin mataimakan gwamnonin CBN.
Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa, Sai dai kuma wani dan majalisa Sanata Muhammed Bulkachuwa ya yi gargadin cewa bai kamata majalisar dattawa ta yi watsi da wannan batu ba saboda mahimmancin dokokin, inda ya ce majalisar wakilai ta gayyaci gwamnan babban bankin kasa CBN Godwin Emefiele da ya gurfana a gaban majalisar domin tattaunawa kan manufofin.
Jaridar Alkiblah ta rawaito cewa, Ranar Larabar da ta gabata ne babban bankin kasar CBN ya fitar da matsayar cire kudi ta hanyar ATM da kuma POS a kan Naira 20,000 a kowace rana.
Babban bankin na CBN ya ce, wannan sabuwar dokar wani shiri ne na kaddamar da sabbin takardun kudi na Naira 200, da Naira 500, da kuma Naira 1,000 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a ranar 23 ga watan Nuwambar 2022.
Ta umurci bankuna da su tabbatar da cewa kudaden da mutane da kamfanoni ke cirewa duk mako ba tare da izini ba, bai wuce Naita 100,000 da Naira 500,000 ba.
