Labarai
2023: Hukumar Zabe INEC Ta Gargadi ‘Yan Siyasa Kan Kalaman Batanci
Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) ta bayar da shawarar yakin neman zabe a tsakanin jam’iyyun siyasa, wanda babu kalaman batanci da tashe-tashen hankula da ka iya kawo cikas ga zaman lafiya a jihar Kano.
Kwamishinan zaben INEC a Kano, Ambasada Zango Abdu ne ya bayyana haka a lokacin wani taron masu ruwa da tsaki kan tattara katin zabe da sauran batutuwan da aka gudanar a jihar.
Ya ce Kano a matsayin daya daga cikin cibiyoyin siyasa a kasar nan ana sa ran za ta jagora abar koyi, wanda hakan ne ya sa taron ya tsara yadda wasu za su yi zabe mai sahihanci da inganci.
A cewarsa, “Idan aka yi la’akari da cewa Kano na daya daga cikin jahohin da siyasa ke kara tabarbarewa, hukumar tana kira ga dukkanin jam’iyyun siyasa da su mayar da hankali wajen yakin neman zabe ba tare da tashin hankali ba, cin zarafi, kalaman batanci da kalaman da basu dace ba da za su iya haifar da rushewar doka da oda.”
Ya kuma kara da cewa hukumar a matakin jiha ta karbi katunan zabe da aka buga wadanda aka yi rajista da kuma canja wuri da gyara ga wadanda suka shiga cikin CVR da ya gabata, inda ya jaddada cewa tuni aka fara rabon katin zabe a ofisoshin karamar hukumar da ke Kano.
Ambasada Zango Abdu ya bayyana cewa rundunar ‘yan sanda a Kano ta kama mutum guda da katin zabe daga karamar hukumar Gabasawa.
“An kama mutumin da katin zabe ya kai 367, kuma an ce na masu kada kuri’a ne daga yankin Yautar, ‘yan sanda sun binciki lamarin kuma an gurfanar da mai laifin a gaban kotu inda aka yanke hukunci.”
A nasa jawabin kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Mamman Dauda wanda ACP Daniel Amah ya wakilta ya tabbatar da aniyar jami’an tsaro na tabbatar da zaben 2023 ba tare da tangarda ba.
