Connect with us

Labarai

Kotu: Ganduje A Shirye Yake Ya Sa Hannu Akan Kisan Abduljabbar – Gwamnatin Kano

Kwamishinan shari’a kuma babban lauyan jihar Kano, Lawan Musa, ya ce gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, a shirye yake ya sanya hannu kan hukuncin kisan malamin addinin musuluncin nan, Abduljabbar Kabara.

Kwamishinan, a zantawarsa da Daily Trust, yana mayar da martani ne kan hukuncin da aka yankewa Abduljabbar da kuma yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan da wata Kotun Shari’ar Musulunci ta Babbar Kotu ta same shi da laifin cin zarafin Annabi da gwamnatin hihar ta yi kararsa.

Musa ya ce gwamnan ya ci gaba da jajircewa wajen ganin ba a tauye doka da oda a jihar ba, inda ya ce hukuncin da kotun ta yanke na tabbatar da korafin da gwamnatin jihar ta shigar a kan malamin, wanda hakan ke nuna babu wanda ke sama da doka.

“Ba za a bar kowa ya karya doka ba tare da daukar matakan da suka dace ba.

“Mun kai shi (Abduljabbar) kotu, muka ba shi dukkan abubuwan da ya kamata domin ya kare kansa, kuma a yau mun gode wa Allah, kotu ta bashi damar kare kansa, kuma ta yanke masa hukuncin da ya dace,” inji shi.

Musa ya kara da cewa: “Kamar yadda (matsayin gwamna) bai canza ba a al’amarin Hanifa, haka nan ma ba ta canza ba.

“Kun san akwai tsare-tsare da yawa da ya kamata a bi kuma mai girma Gwamna a shirye yake; da zarar an kawo masa wannan takardar, zai sa hannu,” ya kara da cewa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvmarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasibomcasibomjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasibomgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet