Uncategorized
Mbappe ba zai bar PSG a Janairu ba –
Kungiyaar kwallon kafa ta PSG ta Yi watsi da rade radin cewa dan wasan gabanta Kylian Mbappe zai sanar da ita cewa zai bar ta a watan Janairu, kuma zai sanar da ita ne kafin sabuwar shekarar.
PSG ta ce lallai tana iya sayar da shi, amma ba a watan Janairu ba, sai a karshen kaka, kuma za ta yi hakan ne idan aka ba ta farashin da ya dace.
Rahotanni na nuni da cewa PSG ba ta tunain rabuwa da Mbappe mai shekaru 24, duba da cewa yana da kwantiragin da zai kai shi har shekarar 2025, sai dai za ta karbi tayi mai gwabi idan har an samu.
Shugaban kungiyar, Nasser Al-Khelaifi yana da yakinin cewa Mbappe yana jin daadin zama a PSG, abin da ya sha nanatawa a lokacin gasar cin kofin duniya.
Saboda haka, Al-Khelaifi ba ya wani shirin rabuwa da dan wasan, wanda ya ce ya mayar da hankali ne a kan lashe kofin zakarun nahiyar Turai.
Shugaban kungiyar, Nasser Al-Khelaifi yana da yakinin cewa Mbappe yana jin daadin zama a PSG, abin da ya sha nanatawa a lokacin gasar cin kofin duniya.
