Uncategorized
Super Eagles ta rikito zuwa Mataki na 5 daga ta 3 a sabon jadawalin FIFA
Tawagar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles ta rikito zuwa matsayin ta 5 a Afrika daga ta 3 da ta ke a baya cikin sabon jadawalin kasashe mafiya iya kwallo da hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA ta fitar.
Sabon jadawalin da FIFA ta fitar ya nuna yadda Super Eagles ta koma matsayin ta 35 a matakin Duniya daga ta 32 da take a baya wanda ke da nasaba da rashin nasarrata a wasannin sada zumuntar da ta doka a baya-bayan nan
Brazil ta ci gaba da zama da 1 a jadawalin na FIFA biye da Argentina a matsayin ta 2 bayan nasararta ta lashe kofin Duniya kana Faransa a matsayin ta 3 sai Belgium ta 4 tukuna Ingila matsayin ta 5.
Matakin rikitowar ta Super Eagles na da nasaba da rashin nasarar data samu zuwa gasar cin kofin Duniya da ta gudana a Qatar bayan shan kaye a hannun Ghana cikin watan Maris din shekarar nan.
