Uncategorized
Kano Pillars: tadauki Yan wasa Arba’in
Kungiyar kwallon kafa ta ta Kano Pillars tace ayanzu haka tadauki Yan wasa Arba’in daza su buga mata kakar wasa ta 2023.
Kamar yanda jami’in Hulda da jama’a na kungiyar Rilwanu idiris Malikawa Garu ya bayyana cewar Yan Arba’in an dauke sune bisa jagorancin Mai Horas da kungiyar Evans ogenyi bayan gwaji da tantan cewa da aka yiwa Yan wasan a filin wasa na Sani Abacha dake kofar mata .
Yakara dacewa Daga cikin yan wasa Arba’in mutum goma Sha takwas nadaga cikin Yan wasan da suka bugawa kungiyar a kakar data gabata,
Sai Kuma mutum biyar Daga karamar kungiyar ta Kano pillers (junior pillers) sauran Kuma an dauko sune Daga wasu kungiyoyin na ketaran kasar nan.
Ayanzu haka Yan wasan zasuje gwajin Lafiyar su kafin Daga karshe Acimma yarjejeniya
Yace duk Wanda aka samu bashi da cikakkiyar Lafiya za’a ajiyeshi Daga cikin Yan wasan kungiyar Arba’in daza su buga kakar wasa ta 2023
