Labarai
Mutum 3 Sun Mutu Sanadin Fashewar Wani Abu A Kogi Gabanin Ziyarar Buhari A Jihar
Mutane uku ne suka mutu sakamakon fashewar wani abu a yankin Okene da ke jihar Kogi.
Tashar Talabijin na Channels ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da safiyar ranar Alhamis din nan a fadar Oyinoyi da ke karamar hukumar Okenne a jihar.
Wannan na zuwa ne sa’o’i kadan da isowar shugaban kasa Muhammadu Buhari domin kaddamar da wasu ayyuka a jihar da ke Arewa ta tsakiya.
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, jami’an ‘yan sanda na sashin yaki da bama-bamai na can a wurin da lamarin ya faru.
Sai dai babu tabbas ko fashewar ta kasance sakamakon tashin bam ne ko kuma hari ne aka kai wa shugaban kasar Buhari.
