Labarai
‘Yan Yahoo Sun Sace Abokinsu Kan Ya Gudu Da Wani Kaso Da Suka Damfari Wani
Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ogun sun ceto wani da ake zargi da damfara a yanar gizo mai suna Haruna Usman, wanda abokan aikinsa suka yi garkuwa da shi saboda rike wasu kudaden da suka yi zambar su.
Wakilinmu ya tattaro cewa dan damfaran da aka yi garkuwa da shi ya bayar da rahoton cewa ya saki Naira 2,200,000 ga wasu mambobin kungiyarsa daga cikin Naira 26,437,950 da ake zargin ya samu daga hannun wani da suka damfara kashe a jihar.
Adadin da wanda ake zargin ya karba yakao kashi 91.7 na jimillar kudaden da suka yi damfara.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abimbola Oyeyemi, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya ce an kama wadannan mutane hudu da ake zargi da damfarar yanar gizo, wadanda aka fi sani da ƴan Yahoo a ranar Litinin.
Ya ce wadanda ake zargin Agbe Simeon, Messiah Nicky, Oladapo Dolapo da Yetunde Shonola an kama su ne a kauyen Orile Imo da ke karamar hukumar Obafemi Owode a jihar.
Kakakin yan sandan ya ce kamen na su ya biyo bayan samun labarin da ‘yan sanda suka samu a hedikwatar sashin Owode Egba cewa an yi garkuwa da Usman a ranar Alhamis din da ta gabata.
Oyeyemi ya ce, “Bayan samun labarin, DPO, sashin Owode-Egba, CSP Popoola Olasunkanmi, ya yi gaggawar tattara mutanensa suka afkawa yankin, inda aka cafke hudu daga cikin wadanda suka yi garkuwa da su, yayin da wasu biyu suka tsere.
