Connect with us

Labarai

‘Duniya Ba Za Ta Manta Da Shi Ba’: Buhari Ya Yi Ta’aziyyar Mutuwar Pele

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajanta wa fitaccen dan wasan kwallon kafa na kasar Brazil, Pele, inda ya bayyana shi a matsayin wanda duniya ba za ta taba mantawa da shi ba kan gudunmawar da ya bayar a wasan.

Pele ya mutu ranar Alhamis yana da shekaru 82 bayan ya yi fama da cutar kansar hanji, in ji danginsa.

Lamarin dai ya janyo ce-ce-ku-ce kan yadda shugaba Buhari ya shiga jerin sunayen shugabannin duniya da ‘yan wasan kwallon kafa da ke ta’aziyyar fitaccen dan kasar Brazil.

“Sai ya huta lafiya. Ya gudanar da rayuwa mai kyau tare da bayar da gagarumar gudunmuwa ga ci gaban kwallon kafa na duniya musamman da kuma harkokin wasanni na duniya baki daya,” in ji Buhari a nasa jawabin, kamar yadda wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kasa Garba Shehu ya fitar.

“Ya kasance yana da karamci mai girma na ruhi da mutunci duk da girmansa a matsayinsa na dan wasan ƙwallon ƙafa na duniya. Ya kuma gina gadoji a tsakanin al’ummomi da kabilu da ma addinai. Ya kasance Jakadan Majalisar Dinkin Duniya maj fatan alheri. Pele ya tafi amma duniya ba za ta taba mantawa da shi ba. RIP.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet