Labarai
Gwamna Ganduje Ya Sanya Hannu Akan Kasafin Kudin 2023
Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje a ranar alhamis din nan ya rattaba hannu a kan Kasafin kudin Shekarar baɗi, wanda Majalisar Dokoki ta Jihar Kano ta Amince da shi.
Gwamnan ya Sanya hannun ne yayin taron Majalisar Zartarwar ta Jihar Kano Wanda ya gudana a dakin taron majalisar dake gidan gwamnatin jiha.
Jim kadan da Sanya hannu a Kasafin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yabawa yan majalisar bisa yadda sukai aikin kasafin kudin ba tare da bata lokaci ba, Wanda hakan zai baiwa Gwamnatin damar fara amfani da kasafin kudin a farkon sabuwar Shekara tun da ya Zama doka.
Gwamnan Ganduje yace bai yi mamakin yadda yan Majalisar suka kammala aikin nasu da wuri ba, Inda yace zai tabbatar an yi aikin da kasafin kudin kamar yadda majalisar ta amince da shi.
Ganduje ya yi alkawarin Ci gaba da baiwa Majalisar yancin cin gashin kanta, ba tare da tsoma baki a harkokin aikin Majalisar ba.
Ya Kuma yaba da yadda Majalisar ta Gudanar da taron Jin ra’ayoyin al’umma akan kasafin, Inda ya bada tabbacin cewa Kasafin kudin zai fi mayar da hankali wajen kammala aiyukan da suka fara don gudun barin bashi mai yawa ga gwamnatin da zata gaje shi, Inda yace kasafin kudin ya samu kari daga Sama da Naira Biliyan 23.
A Jawabin sa tun da fari Shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Kano Hamisu Ibrahim Chidari yace sun Sami nasarar kammala aikin nasu ne akan lokaci Saboda yadda Gwamnan ya gabatar musu da daftarin Kasafin akan Lokaci.
