Connect with us

Labarai

Don Gudanar Da Zaɓe A Rumfunan Zabe 176,846 Akwai Isassun Na’urorin BVAS – INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa tana da isassun na’urar tantancewa ta (BVAS) don gudanar da zabe a rumfunan zabe 176,846 na fadin kasar nan.

Wannan dai na zuwa ne ‘yan makonni kafin babban zaben shekarar 2023 a kasar.

Kwamishinan INEC na kasa, Festus Okoye ne ya bayyana haka a ranar Asabar a yayin wani shiri kai tsaye a gidan talabijin na Channels wani shiri na karshen shekarar 2022 na musamman.

“Na’urar BVAS, wadda muka ce ita ce za ta kawo sauyi dangane da wannan zabe, tana nan. Kuma ina son tabbatar da cewa muna da isassun adadin BVAS da za a yi amfani da su wajen gudanar da zabe a rumfunan zabe 176,846 a fadin kasar nan,” inji shi.

Kwamishinan INEC ya ce sama da ma’aikatan adhoc miliyan 1.4 za a horar da su kan yadda ake amfani da BVAS mai inganci.

“Muna son horar da ma’aikatanmu na wucin gadi tsawon lokaci ta yadda ba za mu sami mutanen da ba su san yadda ake amfani da BVAS ba da kuma zarge ta a kan fasaha da sauransu.

“Muna kuma tattara sunaye da cikakkun bayanai na wadanda za su zama ma’aikatan mu na wucin gadi. Domin zabuka biyu, na kasa da na jihohi, za mu dauki sama da ma’aikatan wucin gadi miliyan 1.4, kuma za mu horar da su,” inji shi.

Jaridar Solacebace ta rawaito cewa An samu labari a baya-bayan nan cewa ’yan siyasa da ke adawa da BVAS na yunkurin yin amfani da kotun shari’a don dakatar da INEC daga amfani da na’urar BVAS da INEC Result Viewing Portal (IReV) a zaben badi amma hukumar zabe ta ci gaba da nanata kudurin ta da kuma muradin ta na ganin an samu nasara don tura sakamakon zaben 2023 na badi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet