Connect with us

Labarai

Hukumar NEMA, Da SEMA Sun Raba Kayan Tallafi Ga Marasa Galihu A Kano

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA tare da hadin gwiwar hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano (SEMA) a ranar Asabar, sun raba kayan agaji ga marasa galihu 406 da wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a karamar hukumar Kiru ta jihar.

Babban daraktan NEMA, Mista Mustapha Ahmed-Habib ne ya bayyana haka a lokacin da yake raba kayan tallafin ga wadanda suka amfana a karamar hukumar Kiru ta jihar.

Ahmed-Habib, wanda ya samu wakilcin Ko’odinetan hukumar NEMA shiyyar Kano, Dr Nuradeen Abdullahi, ya ce kayayyakin tallafin an yi su ne domin a kawo dauki ga wadanda abin ya shafa.

A cewar sa, tallafin na cikin kokarin gwamnatin tarayya na tallafawa wadanda bala’o’i ya rutsa da su a fadin kasar nan.

Ya jera kayayyakin da aka raba wadanda suka hada da: Masara, shinkafa, gero,, Indomie, shinkafa, wake, tumatur, kayan yaji, man kayan lambu, siminti, kusoshi, kwanon rufin da katako.

Shugaban hukumar ya bukaci jama’a da su yi biyayya ga hasashen da hukumar harsashen yanayin sararin samaniya ta Kasa (NiMet) ta yi na ganin an samu ruwan sama domin rage barnar ambaliyar ruwa.

A nasa bangaren, Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Ganduje, ya ce mutane 306 da ambaliyar ruwa ta rutsa da su, da kuma marasa galihu 100 ne suka ci gajiyar buhunan hatsi 7,415 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da su, daga asusun ajiyar kudi na kasa da za a raba a Kano.

Gwamna Ganduje wanda ya samu wakilcin babban sakataren hukumar SEMA, Dr Saleh Jili, ya yabawa shugaba Buhari da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Dr Bola Ahmed Tinubu bisa tallafin kayan agaji ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar.

Ya shawarci al’umma musamman mata masu amfani da itacen wuta da iskar gas da gawayi da su rika kula da wuta tare da raya dabi’ar kashe kayan wutar lantarki a duk lokacin da za su fita ko za su kwanta bacci, don guje wa tashin wuta a lokacin hunturun sanyi

Gwamna Ganduje ya kuma yi kira ga al’ummar yankin da su daina zubar da shara tare da share magudanun ruwa domin kaucewa ambaliya.

Da yake mayar da martani, shugaban karamar hukumar Kiru, Alhaji Muntari Isyaku, ya yabawa hukumar NEMA da gwamnatin jihar Kano bisa wannan karamcin.

Jaridar Justicewatchnews ta rawaito cewa Isyaku ya bukaci wadanda suka ci gajiyar da su yi amfani da kayan cikin adalci.

Sani Lawal-Kiru, a madadin wadanda suka ci gajiyar tallafin, ya yabawa hukumar bisa wannan tallafin tare da alkawarin yin amfani da su ta hanyar da ta dace.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetjojobetjojobet girişholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişjojobetjojobetgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet