Labarai
Murnar Sabuwar shekara: Gwamna El-rufa’i ya yiwa fursunoni afuwa
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya amince da yiwa wasu fursunoni goma sha ɗaya da ke tsare a gidan gyaran hali afuwa a wani ɓangare na murnar sabuwar shekarar bana.
Hakan dai na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga gwaman a kan kafofin yaɗa labarai Mista Muyiwa Adekeye ya fitar da yammacin yau Lahadi.
Sanarwar ta rawaito cewa, afuwar ta shafi fursunonin da suka nuna kyawawan halaye da kuma waɗanda ke fama da rashin lafiya.
Haka kuma sanarwar ta ruwaito cewa, gwamna Malam Nasir El-rufa’i ya buƙaci al’ummar jihar da su ci gaba da kasancewa masu son zaman lafiya.
