Connect with us

Labarai

Asibitin Aminu Kano ya fara bincike kan zargin likita da yin sakacin ruɓewar hannun jariri

Hukumar gudanarwar asibitin koyarwa na Aminu Kano da ke birnin Kano, ya fara gudanar da bincike kan wani likita da ake zargi da yin sakacin da ya yi sanadiyyar ruɓewar hannun wani jariri.

Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Laraba mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun asibitin Hauwa Muhd Abdullahi.

Sanarwar ta ce, asibitin ya girgiza matuƙa da jin wannan labari marar daɗi.

Haka kuma asibitin ya ce, a cikin kimanin shekaru 33 da kafuwar asibitin hakan bai taɓa faruwa ba.

Hukumar asibitin ta kuma jajanta wa iyayen jaririn bisa faruwar iftila’in.

Asibitin ya ƙara da cewa, ya miƙa wa kwamitin da ke bibiyar matsalolin badaqala da sakacin aiki domin faɗaɗa bincike domin ɗaukar matakin da ya dace.

Wannan na zuwa ne bayan da gidan rediyon Premiere FM da ke Jihar Kano ya bankaɗo labarin yadda ake zargin likitan da sakacin ruɓewar hannun jaririn.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantpusulabetvdcasinograndpashabetmarsbahisholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişcasibompusulabetpusulabetmatadorbetonwinimajbetmatbetholiganbetimajbetpusulabetvdcasinosahabetmarsbahismarsbahis girişholiganbetholiganbet girişcasibomcasinolevantcasinolevantsahabetsekabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet