Connect with us

Ilimi

Shugaban ASUU Ya Yabi Gwamnatin Soja Da Cewa Ta Fi Tausayin Malamai

Shugaban kungiyar malaman jami’o’i (ASUU), Fargesa Emmanuel Osodeke ya ce zamanin gwamnatin mulkin soja a kasar nan ya fi tausayawa halin da malamai suke ciki fiye da gwamnatin farar hula a yanzu.

Ya bayyana hakan ne a wajen bikin kaddamar da litattafai 50 na manyan makarantu da marubutan Najeriya suka wallafa a karkashin kulawar asusun tallafawa manyan makarantu (TETFund), a ranar Alhamis a Abuja.

“Na gode kwarai da wannan mai girma minista da dukkan mu da muke halarta taro a yau. Ina so in gode wa abokan aiki na don tayar da batutuwa kuma ina ganin yana da mahimmanci. Zan dan fadi kadan game da menene TETFUND kuma ta yaya ta samo asali?”

“A shekarar 1992 kungiyar malamai ta tsunduma yajin aiki tare da tattaunawa kan yadda muke yi a shekarun baya da Obafemi da abokin aikinmu, bayan mun kammala sai gwamnati ta ce ta yaya za mu iya ba da kudi muka ce ku kalubalance mu, za mu gaya muku yadda za a ba da kuɗin wannan yarjejeniya. Kuma sun kalubalanci ASUU, ba a dauki kwanaki 3 ba, mun fito da wannan tunanin na TETFUND, wanda gwamnatin soja ta yarda da ita. Na ga sojoji sun fi tausayawa… Sai TETFUND ta fara aiki. An sanya hannu kan wannan doka a shekarar 1993. Sai ASUU ta shiga yajin aiki karo na uku domin tabbatar da cewa hukumar ta TETFUND ta samu kudade kuma an saki kudin.”

Dangane da manufar ‘ba aiki babu albashi’ da Gwamnatin Tarayya ke yi kan malaman da ke yajin aiki wanda ya janyo rashin biyan albashin watanni takwas, Osodeke ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kara matsawa gwamnati lamba domin ceto makarantun gaba da sakandare daga durkushewa.

A yayin da ya bayyana TETFUnd a matsayin ginshikin kungiyar, ya yabawa hukumar bisa kawo sauyi a bangaren ilimi na kasa.

Shugaban ASUU ya yi kira da a kara harajin ilimi daga kashi 2.5 zuwa kashi 10 cikin 100 don baiwa TETFUND damar tara kudade don magance kalubalen da ke fuskantar bangaren gaba daya.

A yayin da yake nuna rashin amincewa da halin rashin da’a na wasu manyan kamfanoni da masu hannu da shuni na Najeriya kan biyan harajin ilimi, Osodeke ya ce akwai bukatar a sake mayar da tsarin harajin ilimi domin samar da karin albarkatu ga makarantun gaba da sakandare.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet