Connect with us

Tsaro

Kano: Ƴan sanda sun cafke matasa 61 bisa zargin su da ƙwace wayoyi a taron Tinubu

Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta yi holin wasu matasa su 61 da ta cafke bisa zargin su da ayyukan ta’addanci ta hanyar ƙwacen wayoyin mutane a ranar Larabar makon nan.

Rundunar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ta SP Abdullahi Haruna, ya fitar a daren Alhamis ɗin nan.

Sanarwar ta ce, an cafke matasan ne ɗauke da makamai da miyagun ƙwayoyi yayin gudanarda taron bada tutar ƴan takarar jam’iyyar APC a filin wasa na Sani Abacha da ke Ƙofar Mata.

Ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ga manema labarai a yau.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta cikin Sanarwar, ya kuma ce an samu matasan da makamai da suka haɗa da wuƙaƙe guda 33 da adda 8 da almakashi guda 4 sai da tabar Wiwi sinƙi daya da sauran kayayyakin maye.

Sanarwar ta kuma ruwaito cewa Kwamishina ƴan sandan Kano Mamman Dauda ya bayar da umarnin gurfanarda matasan da ake zargi a gaban Kotun Majistri dake Normans land a yau domin yanke musu hukunci.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet