Labarai
An Kama Wani Mutum Bisa Laifin Yi Wa Wata Mata Fitsari A Cikin Jirgin Sama
An kama wani korarren shugaban babban bankin Amurka Wells Fargo da ake zargi da yi wa wani fasinja fitsari a cikin jirgin Air India, kamar yadda kakakin ‘yan sanda ya fada a ranar Asabar.
Shankar Mishra, tsohon mataimakin shugaban kula da ayyukan bankin na Indiya, ya kasance gujajje daga hukumomi bayan da wata tsohuwa ta koka game da abin da ya faru a watan Nuwamba ga mahukuntan kamfanin.
Kafofin yada labarai sun ce Mishra ya kashe wayarsa amma ya ci gaba da tuntubar abokansa ta kafafen sada zumunta kuma ya yi cinikin katin waya a babban birnin IT na Bangalore da ke Indiya, wanda ya ba da wurinsa.
Rahotanni sun ce an kawo shi babban birnin New Delhi inda ‘yan sanda ke gudanar da bincike kan zargin.
Mai magana da yawun ‘yan sanda a Delhi ya tabbatar da kama Mishra ga kamfanin dillancin labarai AFP ba tare da ba da wani cikakken bayani ba.
Wells Fargo ya ce a ranar Juma’a an kori ma’aikacin nata bayan zargin “mai matukar tayar da hankali” ya fito fili.
An bayar da rahoton cewa Mishra ya abun ne a lokacin da yake tafiya daga New York zuwa New Delhi a ranar 26 ga watan Nuwamba lokacin da ya zare wandonsa yayi fitsari a kan wata mata mai shekaru 72 da ke zaune a fannin kasuwanci.
Kamfanin jirgin ya ce ya gaza shawo kan lamarin yadda ya kamata kuma yana nazarin manufofinsa na shan barasa a lokacin tashin jirgi.
“Air India ta amince da cewa za ta iya magance wadannan al’amura da kyau, ta sama da kasa kuma ta kuduri aniyar daukar mataki,” in ji babban jami’in gudanarwa Campbell Wilson a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.
Kamfanin jirgin, wanda kamfanin Tata Group ya siya kwanan nan bayan shekaru da dama a karkashin ikon gwamnati, ya fuskanci kakkausar suka kan yadda ya tafiyar da korafin matar.
