Connect with us

Labarai

Rashin Tsaro: Gwamnatin Tarayya Ta Baiwa ‘Yan Nijeriya Tabbaci Za A Yi Zabe

 

Duk da barazanar tsaro, gwamnatin tarayya ta baiwa ‘yan Najeriya tabbacin cewa zabukan 2023 zasu gudana a fadin kasar.

Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed ya ba da wannan tabbacin a ranar Talata a wajen taron duba gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari karo na 17 daga 2015-2023.

“Bari in yi amfani da wannan dama domin amsa tambayoyi daga manema labarai kan wani rahoto da ake ta yadawa, wanda wani jami’in INEC ya bayyana cewa zaben 2023 na fuskantar babbar barazanar sokewa saboda rashin tsaro,” inji shi.

“Matsayin Gwamnatin Tarayya ya rage cewa za a gudanar da zaben 2023 kamar yadda aka tsara. Babu wani abu da ya faru da zai canza wannan matsayi. Muna sane da cewa INEC na hada kai da hukumomin tsaro domin ganin an gudanar da zaben cikin nasara a fadin kasar nan.

“Hukumomin tsaro sun kuma ci gaba da tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa suna bakin kokarinsu wajen ganin an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali. Don haka, babu wani dalili na fargaba.”

Tabbacin na ministan ya biyo bayan kashe-kashen da ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda suka yi a sassa da dama na kasar.

A ranar Litinin din da ta gabata ne hukumar zabe ta kasa (INEC) ta yi tsokaci kan tabarbarewar harkokin tsaro a fadin kasar nan da kuma tasirinsu a zaben 2023 mai zuwa.

Duk da kokarin da hukumomin tsaro da gwamnatin tarayya suka yi, ‘yan bindigar sun ci gaba da kai hare-hare a ofisoshin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), jami’an tsaro da sauransu, inda suka kashe mutane da dama.

Jaridar Alkiblah ta rawaito cewa Dangane da lamarin, INEC ta koka da cewa an kai hare-hare sama da 41 a ofisoshinta a jihohi 14 tun bayan zaben 2019, inda yankin Kudu maso Gabas ya hare-hare suka fi kamari da guda 13.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet