Labarai
2023: Kar Ku Tsoma Mana Baki A Zabenmu, Buhari Ya Gargadi Kasashen Waje
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada gargadin sa ga wakilan gwamnatin kasashen waje da kada su tsoma baki a zaben 2023 mai zuwa.
Buhari ya yi wannan gargadin ne a lokacin da yake karbar wasiku daga jakadun kasashen Switzerland da Sweden da Jamhuriyar Ireland da Masarautar Thailand da Jamhuriyar Senegal da kuma Jamhuriyar Sudan ta Kudu a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Shugaban ya ce: ‘’Ina rokon ku da ku kasance masu bin tsarin diflomasiyya don tabbatar da cewa ayyukanku sun kasance a cikin iyakokin aikin ku yayin da kuke sa ido kan yadda za a gudanar da zabuka da kuma yadda babban zaben ke gudana.
“Ina yi muku fatan alheri a cikin rangadin ayyukanku daban-daban kuma a lokaci guda kuma ina ƙarfafar ku da ku ɗauki lokaci don jin daɗin yanayi da al’adu na musamman a hannunku yayin da kuke tafiya a cikin ƙasarmu.”
Buhari ya bayyana cewa Najeriya na hada kai da kungiyar ECOWAS domin magance matsalar rashin tsaro a yankin yammacin Afrika tare da aiwatar da dabarun dakile yawaitar sauye-sauyen da ake samu a gwamnati.
Ya bukaci hadin kai da hadin gwiwa daga kasashen domin shawo kan kalubalen da ke yammacin Afirka.
Jaridar Solacebace ta rawaito cewa Shugaba Buhari ya gayyaci kasashen da aKe abokantaka da su ‘’tallafawa kokarin da ake na magance matsalar rashin tsaro, yaki da cin hanci da rashawa, da habaka tattalin arziki, da kokarinmu na inganta shugabanci na gari.
Ya shaida wa Jakadun cewa, ko shakka babu Najeriya na da kyakkyawar alaka da hadin gwiwa da kasashensu, inda ya yaba da rawar da magabata suka taka, wadanda suka nuna himma da jajircewa wajen ciyar da wadannan abubuwa gaba.
Ya kara da cewa: ‘’Saboda haka ina da yakinin cewa nadin da kuka yi a bayyane yake da gangan don gina nasarorin da magabatanku suka samu domin ciyar da dangantakarmu zuwa ga mahimmiyar nasara.
“Yayin da kuka zauna kan aikin diflomasiyya, ina fatan za ku yaba da bambance-bambancen siyasa, zamantakewa da tattalin arziki da al’adu wadanda su ne alamomin al’ummar Najeriya.”
