Connect with us

Labarai

Gwamnan Jihar Neja Ya Sanya Dokar Hana Fita Biyo Bayan Rikicin Da Ya Barke

 

Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani-Bello, ya sanya dokar hana fita daga garin Lambata da ke karamar hukumar Gurara a jihar sakamakon wani kazamin rikici da ya kai ga kashe Hakimin kauyen Mohammed Abdulsafur.

Jaridar Solacebace ta rawaito cewa Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Ahmed Matane ya fitar ranar Lahadi a Minna.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa ya bayar da rahoton cewa, wasu ‘yan daba sun kashe hakimin kauyen Lambata a ranar Asabar a wani rikici da ya barke.

Mista Sani Bello ya bayar da umarnin sanya dokar hana fita a garin daga karfe 6.00 na dare zuwa karfe 6.00 na safe, daga ranar Lahadi, har zuwa wani lokaci.

Ya ce, sanya dokar ta-bacin ya zama dole domin a taimaka wa jami’an tsaro wajen daidaita al’amura, da ceton rayuka da kuma maido da doka da oda.

A cewar gwamnan, gwamnati ta yi Allah wadai da tashe-tashen hankula da rashin bin doka da oda da suka faru a garin Lambata.

Ya yi kira ga al’ummar yankin da su ba jami’an tsaro hadin kai domin dawo da zaman lafiya a garin, ya kuma bukaci jami’an tsaro da su tabbatar da aiwatar da dokar hana fitar. NAN

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet