Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano Ta Kori Wasu Mata Biyu Daga Gidan Marayu Na Nasarawa

 

Gwamnatin jihar Kano ta yi watsi da rahoton zargin cin zarafin yara da jami’anta suka yi a gidan yara na maratu da ke Nasarawa.

Kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban al’umma ta jihar, Dakta Zahra’u Muhammad-Umar, ta yi watsi da rahoton yayin da take zantawa da manema labarai a Kano ranar Lahadi.

“Wasu masu yin barna ne suka hada labarin don bata sunan gwamnatin jihar. Ba a yarda mu ci gaba da adana yara masu girma sama da shekaru 18 a gidan marayu bisa doka ba.

“An nemi wasu manya biyu daga gidan marayun, Ladidi da Saudat da su bar gidan marayun tunda yanzu sun zama manya.”

Muhammad Umar ya bayyana cewa matan biyu, daya wadda aka saki, dayar kuma ta aurar da ‘ya’ya uku, sun ki barin gidan ne kuma suna amfani da dabarun bata wa kwamishiniyar da kula da gidan marayun suna.

“Dukkan biyun sun je gidan rediyo sun yi zargin cewa ana lalata da yara a gidan, ana sayar da su kuma an mayar da su gidan reno ba bisa ka’ida ba, da sauransu yayin da suke neman tausayawa daga jama’a.”

Ta ce gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti da zai binciki zargin da aka gano na karya ne, inda ta ce kwamitin ya yanke shawarar cewa Ladidi da Saudat su bar gidan saboda sun haura shekaru 30.

“Lokacin da na zama kwamishina, na tausaya wa manya, na zama uwa gare su, na sanya wasu daga cikinsu a manyan makarantu.”

Ta ce gwamnatin jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarinta na daukaka darajar rayuwa a tsakanin ‘yan kasa ta hanyar manufofi da tsare-tsare.

A nasa bangaren, shugaban kwamitin renon reno na jihar Kano, Alhaji Kabiru Zubairu, ya ce kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa ya kunshi mambobi tara da za su kula da renon yara.

Kwamitin ya hada da Jami’in ‘Yan Sanda a matsayin Sakatare, REPA, Darakta (Yara a Ma’aikatar), Masanin Ilimi daga Ma’aikatar Ilimi, Jami’in Shari’a, Likita da Jami’an Jin Dadin Jama’a a matsayin mambobi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet